×
Home: Mobile Home: Original Style Christian Netflix Jewish Stories X-Witch X-Muslim MP3 Bible Bible Movies Gospel Videos Godly Movies CBN Videos Kids Videos Worship Music Vids for New Believers Random Video Ask AI Bible Questions What's New
  Kat Kerr   Anna Rountree   Mary Baxter   Several #1   Several #2   Choo Thomas   Ian McCormack   Burpo   I saw His Glory   7 Colombian Youths   Heavenly Blood   Heaven Testimonies
  Lazarus   Bill Wiese   Mary Baxter   Dr. Rawlings   J. Perez   Hepzibah   Ptr. Park   7 Columbian Youths
  Atomic Prayer   Prayers that ROUT demons   Courts of Heaven   Warfare + Blessing   Healing   Declaration   101 Decrees   Healing Decrees Capps   Prayers to Cover Everything   Tongues   Rosary   Artic Fire   Why Should We Pray?   Why Bother
  MP3 Bible   10 Commandments   Learn Bible in 24 Hours   40 Spiritual Lessons   Alpha   Foundations   Bible Commentaries   Book of Mormon   Temple Study   Red Letters   Divine Healing Training   God Story   Gap Theory   Creation to Christ   Book of John   Kids Bible Cartoons   Derek Prince Teaching   Jesus Film   Digital Bible   Bible Codes ELS   Memorize the Bible   Bible Games
  Passion of Christ   New Jesus Film   Introduction   Names of God   Jesus IS...   Jesus Film   That's My KING   Father's Love Letter   Celestial Hug
  Warfare Training 1   Warfare Training 2   Casting Out demons   They Shall Expel demons   Combat   Examples   Warrior King   Exorcism   Prayer   Deliverance Song   Ask Him   demonology   Clarita   NUWI
  Final Quest   The Call   Tommy Hicks   3 Days   Angel Song   The Prison   H.A.Baker
  Best #1   Best #2   Generals   Ramirez   Supernatual Stories   Spiritual Food   Dale Black   Bishop Kelley   Sid Roth   Fatima   Richard Sigmund   Gary Wood   Roland Buck   Rees Howells   Baptized by Fire   Todd White   Gary Beaton   Victor Marx   False Prophets   Akiane   Theo Nez   Milton Alvarez   Nun's Story   Retha McPherson   Tomas Welch
  Booth's Vision   Frank Jenner   Hell's Best Kept Secret   EE-Taow   Manifesting Power   LivingWaters   Atheist Delusion   Using AI for Jesus   Sharing w/ Muslims   Sword + Serpent
  Revival Hymn   Jesus in China   Freemason Curruption   Modern Child Sacrifice   the WAR on Children   XGay   Transformations   Ark of Covenant   Soul Ties   Last Reformation   Noah's Ark Found   Does GOD Exist   Political Issues   Fake Mountain   7 Mountains   ID vs Evolution   Bible Science   American History   China Records   Case: Creator   Case: Christ   Case: Faith   Little Lessons   Deadly Mistakes   Enemies Within   Chinese Characters   Global Warming   The Final Frontier   Understanding Israel   Testing Joseph Smith   Targeting Kids
  X-Muslim   Journey of Hope   Islam Rising   ACT   Jihad   Best Muslim Story   Enemies Within   Answering Islam   Killing for Heaven   Killing the Infidel
  Downloadable MP3 Worship Music   Online Worship Music   Practice Presence of God  DivineRevelations University   Free Posters   Christian Pictures   Kids Christian Cartoons   Bible Trivia   End Times Visions   Fractal Praise   Soaking Music   Communion Verses   Bobby Conner   Brother Yun   Contorting Jesus   Civil War   Prayer Tank   Fiscal Cliff   Understanding Economics   Who takes the Son   Christian GPTs
  All Languages   Afrikaans   Albanian   Amharic   Arabic   Bengali   Bulgarian   Burmese   Cambodian   Catalan   Chinese   Czech   Danish   Dutch   Farsi   Finnish   French   German   Greek   Gujarati   Hausa   Heberw   Hindi   Hungarian   Indonesian   Italian   Japan   Kannada   Khazanah   Korean   Laos   Malagasy   Malayalam   Malaysian   Marathi   Mongolian   Nepali   Norwegian   Oriya   Polish   Portuguese   Punjabi   Romanian   Russian   Somali   Samoan   Serbo_Croatian   Sinhala   Slovak   Slovenian   Spanish   Swahili   Swedish   Tagalog   Tajik   Tamil   Telugu   Thai   Tongan   Turkish   Ukrainian   Urdu   Uzbek   Vietnamese
 About  Disclaimer  Phone# USA 425-610-9216  [email protected]  Donate
Follow on YOUTUBE  YouTube Follow on Facebook  Facebook Follow on X/Twitter  X/Twitter Follow Podcast RSS  Podcast  RSS Follow on Instagram  Instagram Follow on TikTok  TikTok
  PDF Library   Believer's Authority   Heavenly Man, Yun   Torch + Sword   The Harvest   Faith Shoemaker's Vision   Daughter of Sacrifice
Something Funny... 2nd Page, Older Material
×






Menu / Home
Menu / Home

HTML Bible Gospel Go The Prophet's Story Passion of the Christ The Jesus Film 4 Spiritual Laws
Ruya Game Da Aljanna     WAHAYI AKAN JAHANNAMA     Muslim Dreams/Mohammed  MP4 Hi Low      LOKACI NA WUCEWA DA SAURI

LOKACI NA WUCEWA DA SAURI
Shaidar ziyara Yesu Kristi Ga Victoria Nehale

PDF  DOC

[Victoria's Website]  English  Spanish  Korean  Samoan  Bahasa Malaysia  Japanese  Portuguese  Indonesian  Tagalog  Swedish  French  Arabic  Romanian  Hausa  Swahili  Burmese  Malagasy Amharic

An haife ni na kuma yi duk rayuwa ta a Namibia, na karbi Yesu ya zama mai cetona a ranar shida ga watar Faburairu ta shekarar 2005. Ubangiji Yesu Kristi ya bayyana abubuwa masu yawa ta ruhaniya gareni, wadda ta hada da ziyarata zuwa jahannama. Ubangiji Ya umurce ni in bada labari na ga mutane; Ya kuma yi mani galgadi kada in kara kome ko in rage kome daga abubuwan da Ubangiji Yesu Kristi Ya nuna mani ko kuwa Ya fadi. A karshen shekarar 2006, lokacin da nake rubuta wannan littafi, Ubangiji Yesu Kristi Ya ziyarce ni sau talatin da uku (33) ke nan. Kafin ya tafi a kowacce lokacin ziyarar sa ya kan ce mani: LOKACI NA WUCEWA DA SAURI.

TAFIYA TA FARI ZUWA JAHANNAMA

A ranar ashirin da uku (23) ga watar Yuli ta shekarar 2005, na yi tafiya daga Ondangwa garin da na ke zama da kuma aiki zuwa kauye na, wadda tafiyar minti talatin ne domin in yi wasu ‘yar kwanaki a karshen makon da iyaye na. A hanya, jiki na ya bani cewa wani abu zai faru. Na isa gida a lokacin da mutane suke girkin abincin dare wato kamar karfe shida na yamma. Ina kwance a kan wata tsohuwar kyalle a cikin madafi tare da sauran ‘yan uwa na. Wasun su na wakokin majami’a, karaf daya na ji wani nauyi ya sauko mani, nauyi irin ta Ruhun Ubangiji, sai jiki na ya mutu, ashe iko ne na Ubangiji ta ke kai na. Sai na ga wani mutum sake da doguwar farar riga daure da igiya a kunkumin sa, haske kewaye da shi yana tahowa wurin da nake kwance. Yana da kamanin mutanen kasashen gabas ta tsakiya, ban iya kallon fuskar sa ba domin yana cike da daukaka. Ya yi mani magana a cikin murya cike da kauna da iko.

Ya mika hannunsa ya daga ni daga inda nake kwance sai karaf daya na ga kamanin na ta canza na yi kama da lokacin da nake da shekaru sha-takwas. Ina sake da fararen tufafi, koda shike tufafina ba kamar na sa bane. Na sa yana da yalki da kuma tsantsi, kamanin tufafinsa bazan iya kwatanta wa ba.

A cikin murya mai dadi cike da kauna “Victoria ki biyo ni, zan nuna miki abubuwan da baki taba gani ba a duk rayuwar ki, abubuwa ma su ban tsoro.” Ya rike hannun dama na sai muka fara tafiya a tsarari, mu ka ta hawa sama. Na gaji bayan mun yi tafiya na dan lokaci, sai na ce masa bazan iya cigaba da tafiyar ba, na roke shi ya bar ni in koma. Amma ya dube ni da tausayi ya ce: “Ba ki gaji ba tukuna, idan kin gaji zan dauke ki saboda haka mu cigaba da tafiya, salama a gare ki, mu je”

Mun isa wata Hamada wadda babu abu mai rai a wurin ba za a kuma kwatanta da kowace irin Hamada ba a duniya. Babu itace ko ciyawa ko wani abu mai rai a wannan wurin.

Da muka isa wata babbar kofa sai ya ce mani: “Victoria za mu shiga ta wannan kofa, abubuwan da za ki gani zai tsorata ki, zai kuma dame ke amma ki sani fa ina tare da ke, zan lura da ke, ba zan bar kome ya same ki ba. Sai ki bude idanunki ki dubi duk abinda zan nuna ma ki.” Na ji tsoro kwarai, har ina hawaye, ina ta rokon sa ya mayar da ni, na ce masa bazan iya shiga wannan wuri ba domin abubuwa da na gani daga kofa. Sai ya dube ni ya ce: “Salama a gare ki, ina tare da ke, dole ne mu shiga ciki domin lokaci na wuce wa.”

Mun shiga ta wannan babban kofa, bazan iya kwatanta azaba da abubuwan tsoro da ke wannan wuri ba. A duk duniya babu mumunar wajen zama da za’a kwatanta da wannan wurin. Babban wuri ne wadda a gani na yana dadda buduwa a kowanne minti. Wannan wajen na da duhu, baki kirin ga kuma zafi wadda ba za a iya auna gwada wa ba. Ban ga wuta na ci ba, amma zafin ya fi kowanne irin wuta zafi, kudaje masu girma dabam-dabam, masu launin kore, baki, ruwan toka da duk kowanne irin kuda za a samu a wurin. Akwai wasu irin tsutsotsi, suna nan guntaye, manya-manya, bakake. Tsutsotsin su na hawa jikin kome, har ma sun hau jikin mu ma. Ga kuma kudaje ko ta ina.

Warin wannan wajen yana nan kamar rubbaben nama, amma ba wani rubbaben nama da na taba gani da ya kaishi wari a duk rayuwata. Wurin na cike da kuka da cizon hakora da kuma dariyar mugunta na aljannu da suke wajen

Abin bakin cike game da wannan waje shi ne yana cike da mutane, mutanefiye abin a kirga. Jikin mutanen kasusuwa ne amma na gane wasu dangina da wasu ‘yan kauye na a wurin. Kasusuwan su suna nan a bushe ma su launin toka, su na da kuma hokora dogaye masu tsini kamar na naman daji. Mutanen su na da manyan bakuna da dogayen harsuna jajaye. Hannayen su da sawayen su suna da dogayen farsu kamar kusoshi, wasu suna da ma wutsiya da kaho.

Aljannun da suke yawo a cikin mutanen su na da kamanin zamo, suna da kuma kafafuwa hudu, su na nan sake a cikin wannan wajen, suna cike da murna da farinciki, suna rawa da tsalle suna kuma ba wadan nan mutane azaba. Mutanen suna zama abin tausayi, ba su da mai taimako, ba su da kuma begen mai taimako. Mutanen suna ihu, suna kuka suna cizon hakora domin azabar da suke ciki.

Mutanen da suke wannan wurin ba abin a kirga ba, amma ma fi yawan su mata ne; an raba su kashi- kashi amma duk da haka ba za a iya kirga mutanen ba domin yawan su.

Mutumin nan ya kai ni zuwa wata sashen mutane da suke ta gabas, ya dube ni ya ce: “Victoria, wannan sashen su ne mutanen da sun ki yafewa. Sau dayawa a kuma hanyoyi dayawa ina gaya masu su yafe wa juna amma sun ki ji na. Na yafe masu zunuban su amma sun ki su yafe wa wasu laifofin su. Lokaci ya wuce masu, yanzu sun sami kansu a nan. Za su kasance a nan suna girbin abin da su ka shuka. Yana mini zafi yadda nake ganin su a nan domin ina kaunar su.”

An kuma kai ni zuwa wata sashen mutanen. Mutumin ya ce mani wannan mutane ana bin su bashi ne, an sake kasa su zuwa wasu kananan kashi: kashi na farko su ne wadan da suna da halin biyan bashinsu amma sun ki biya, suna ta turawa sai gobe, sai mako mai zuwa, sai shekara mai zuwa, har lokaci ta wuce masu suka sami kansu a nan. Za su kasance a nan har abada suna girbin abin da sun shuka.

Kashi na biyu kuma sune mutanen da suke da bashin da ba za su iya biya ba, suna da niyyar biyan bashin su amma suna tsoron fadin gaskiya cewa ba su da shi, suna zaton za a ki su, za a kuma kulle su. Mutumin ya ce: “Babu ko dayan su da ya zo neman taimako a wuri na, da na taimaka masu, amma sun yi amfani da hikimar su da kuma iyawar su wadda bai taimake su ba. Lokaci ya wuce masu, yanzu za su kasanche a nan har abada suna girbin aikin hannuwan su.”

Sai ya ce mani “Kashi na uku suna da bashin da ba za su iya biya ba, ba su kuwa gaya mani cewa suna da bashin da ba za su iya biya ba, da na taimake su. Su ma sun yi amfani da tunanin su da hikimar su wadda bata taimake su ba. Yanzu sun sami kansu a wannan wajen za su kasanche a nan suna girbin aikin hannuwan su. Ina bakin cikin ganin su a nan domin ina kaunar su sosai.

A kashi na farko na ga wasu mata wadda dangina ne na kusa, akwai wata dangina ma mai shekaru goma-sha-biyu a wannan kashin. A kashi na biyu na ga wasu dangina da kuma wani pasto wanda na sani. Saurayina, Jakes wadda ya kashe kansa domin na karbi Yesu Kristi ya zama mai ceto na yana wannan kashi na biyun. Na kuma ga wasu makwabta na a kashi-kashin mutanen nan.

Na gane wasu mutanen da na sani kafin mutuwar su, su ma sun gane ni. Dangina sun bata rai da gani na, suna ta yi mani maganganu marasa dadi, suna ta zagi na. Wani a cikin su ya ce ni ban isa in yi tafiya da wannan mutumin ba. Su na ta fadin abubuwan da na ke yi a da kafin in karbi Yesu cikin rayuwa ta. Abubuwan dasu ke fadi game da ni gaskiya ne, saurayi na Jakes yana ce mani ni nasa ne, ya kamata in zo wajen da yake domin ni ma na yi irin zunuban da ya yi. A farko dai paston nan ya yi murnan gani na amma da ya ga wadda yake tare da ni, fuskarsa ya canza, shi ma ya fara zagi na. Mutumin da ya ke da ni ya ce kar in damu da abubuwan da su ke fadi, ba su san abin da su ke yi ba.

Rai na ya baci, na kuma tsorata kwarai, jikina yana ta rawa, na gagara tsayawa, ina ta kuka. Sai mutumin ya rungume ni, ya ce, “salama gareki Victoria.” Da ya rungume ni sai na ji sabon karfi, sai na daina jin tsoro domin na san yana tsaro na. Sai ya ce mani mu bar wannan wurin mu koma. Mutumin ya kalle ni ya ce: Victoria na nuna ma ki kome, sai ki zaba wane kashi ki ke so ki zama? Sai ki gaya wa mutane abinda ki ka ji, ki ka kuma gani kar ki kara ko ki rage kome.”

Na tuna mun bar wannan wajen tare amma ban san lokacin da na rabu da shi ba, sai dai na bude idanu na na ga ina kwance a cikin jikina a asibitin Oshakati. An saka mani ruwa a hannun hagu na, mamana da wasu makwabtan mu a kauye suna cikin dakin, suna kallo da mamaki. Daga ganin fuskar mamana, na gane ta yi ta kuka. Na tambayi nas (mai aikin jinya) da take tare da ni ko ta san abinda yake dami na? Sai ta ce a cikin wasa, “watakila an dawo da ke domin wani abinda ki ka yi da ba daidai ba, ya kamata ki tuba”

Nas din ta na kokari ta yi mani magana da fara’a amma ta na tsoron zuwa kusa da ni. Sai na ce ma ta, ta kira mani likita.

Da likitan ya zo, ya ce bai san abinda ke damu na ba. Da farko ya zata ina da zazzabi amma da aka yi mani gwaji ba a ga kome ba. Likitan ya gaya mani cewa jiki na da zafi, hauhawar jini na kuma ya yi kasa sosai, bai gano dalilin haka ba tukuna. Ya ce ba abinda zai iya yi mani, ba zai kwantar da ni a asibiti ba domin ina da lafiya. Ruwan da su ka sa mani baya tafiya da farko san da na falka sa’anan ya fara aiki. Likitan ya ce wa nas ta sa mani wani ledar ruwa idan na farkon ya kare domin in sami karfin tafiya gida.

Na tsorata kuma na dinga kuka domin abinda na gani a wannan wajen: na yi ta jin warin wannan wajen, ina ta ganin abubuwan da na gani a wannan wajen a cikin ido na. Na gagara barci, duk jiki na ya na ta ciwo. Kafafu na su na ciwo kamar an cire an sake mayar da su, ina zawo, kai na yana ta ciwo, jiki na gaba daya ya mutu.

Sai na kudurta a zuciya na bazan gaya wa kowa abinda ya faru ba, domin ina zaton waye zai yarda? Menene mutane za su fada game da ni? Na yi ta fada wa zuciya ta cewa ba zan gaya wa kowa ba. Bayan kwana uku wata mallamata ta kira ni domin ta tambayi lafiya na, domin na bata sako cewa ta yi mani addu’a. Kamin in hankara ina gaya mata abin da ya faru da ni. Bayan da na yi nisa da bata labarin sai na tuna cewa ba zan gaya wa kowa ba amma Allah mai iko duka ne, idan Yana son abu ya faru, dole ne ya faru. Na gane cewa lallai Allah Yana so in gaya wa wasu wannan labarin.

A ranar 19 ga watar Agusta na ji hannun Ubangiji a kaina sai jiki na ya mutu, jiki na yana ta rawa, ina ji kamar wutar lantarki yana yawo a jiki na. Da yamma, na ga wata haske mai karfi ta shigo dakin da na ke, wannan mutumin na cikin hasken. Sai ya zauna a kujera a gefen gado na, ban san inda kujera ta fito ba, amma kujerar na wajen a lokacin da ya shirya ya zauna. Kyakkyawar kujera ce wadda aka yi ta da zinari. A kowanne kafa akwai tauraro wadda aka yi ta da azurfa kewaye da zinari. Akwai irin wannan tauraron a bayan kujerar. Kafafuwan kujerar su na nan kamar ta tayar kafar keke.

Bayan ya gaishe ni sai ya ce mani ya san ina da tambayoyi game da wanene shi, ya kuma zo domin ya bayyana mani kansa sannan kuma ya bayyana mani abubuwan da na gani. Ya ce: “Ni ne Yesu Kristi, mai ceton ki, idan kina shakka ki dubi hannaye na. Wannan wajen da muka je jahannanma ne.” Da na dubi hannunsa na ga tabon inda aka soka mishi kusa.

Abokina, jahannama na nan da gaskiye, ba zato ko tunanin wanni ba ne, ba kuwa waje mai dadi ba ne. Ba a yi jahannama domin mutane ba, an yi shi ne domin shaidan da aljannun sa. Wajen da ya kamata mu zauna shi ne a sama tare da Yesu, amma dole ne mu karbi Yesu tun da wuri. Yau in ka ji muryar Sa, kada ka taurare zuciyar ka, ka karbe Shi ya zama Ubangijin ka da mai ceton ka yau domin ka zauna tare da Shi har ababda. Jahannama mummunar waje ne, cike da bakin ciki, wajen azaba ne da kuka da cizon hakora. Shaidan yana so ya dauki mutane dayawa zuwa jahannama, kada ka bashi hadin kai amma ka hada kai da Yesu, Shi zai ba ka rai na har abada.

Ban gane dalilin da Ubangiji ya ce mani in zaba tsakanin wadannan kashi-kashi da su ke jahannama bayan na karbi Yesu. Na karbe Yesu cikin rayuwata amma yana ce mani ko in so ko ba ni so in je jahannama. Ban fahimta ba, sai na fara addu’a ina rokon Allah Ya bayyana mani abinda yake nufi, Ya ke kuma bukata in yi. Ubangiji ya bayyana mani cewa na ki in yafe wa wata ‘yar uwata. Da kuma wata dangina na kusa. Sai na roki Allah ya yafe mani domin na ki in gafarta wa ‘yar uwata, na roke dukan su gafarta mani cewa ba zan cigaba da rike su a zuciya ba.

Ubangiji ya tunashe ni cewa akwai lokacin da na nemi aikin koyarwa da takardan kalmala makarantan difloma wadda ba nawa ba ne. Ya ce mani a gareshi wannan bashi ne da kuma sata. Na kudura a raina in yi abinda ya kamata, na kuma roki Ubangiji ya taimake ni cikin wannan damuwan sa’an nan kuma Ya nuna mani hanya mafi saukin fita daga wannan damuwa domin wannan babbar laifi ne wadda za a iya kulle ni a kurkuku. Ya ce mani in je sashi na ilimi in fada abin da na yi, ina shirye da cewa za a kulle ni a kurkuku amma Ubangiji Ya nuna mani alherinsa da na gaya wa ma’aikatan sashen ilimin, sun ce mani in biya gwamnati albashin da na karba. Sun ce ba za su kai ni kotu ba domin sun ji mamakin shaidan da na yi. Ubangiji mai cika alkawali ne, Yana kuma daukaka Maganarsa. Idan kana cikin wata hali irin nawa, ina so in karfafa ka cewa ka yi abinda ya ke daidai, ko da menene sakamakon. Idan an kulle ka ba har abada ba ne. Idan an kwatanta shi da azabar rabuwa da Ubangiji Allah har abada, babu kunya ko wahala da ya kai shi. Jahannama ba waje mai kyau ba ne, gwanda ka karbi hukuncin Allah yanzu kafin ya yi latti. Bai kamata mu ji tsoron hukuncin Allah ba domin muna lokacin alherin Sa ne, mu bar Shi ya share laifofin mui tun mu na da rai domin babu tuba a kabari.

TAFIYATA TA BIYU ZUWA JAHANNAMA

A ranar sha-takwas (18) ga watar Oktoba, na tashi da karfe biyar da rabi (5:30) na safe amma na gagara zuwa wajen aiki, ina jin jiki na ya mutu kamar na bugu. Na gagara juyawa ko motsi a kan gado na, Ruhun Ubangiji ya sauko cikin dakin, jikina na rawa ina ji kamar wutar lantarki a chikin jiki na. Ubangiji Ya zo Ya dauke ni a misalin karfe takwas na safe domin a lokacin da na duba agogo karfe bakwai ne da minti arba’in da takwas (7:48), kuma jim kadan bayan wannan lokacin ne ya iso. Ya yi mani gaisuwa, sai Ya ce mani mu tafi domin lokaci na wucewa. Na tashi a tsaye na fara tafiya, hanyar da muke bi daban ne da wadda mun bi kwanakin baya, ko da shike kafafuwar mu na tafiya amma tafiyar mu kamar mu na tashine a tsarari. A cikin tafiyar mu Yesu Ya ce mani kowanne irin zunubi bashi da kyau, babu kuma babba ko karamar zunubi. Kowanne irin zunubi yana kai ga mutuwa ko babba ko karami. Ubangiji Ya ce mani zamu je jahannama ne kuma. Ya tambaye ni ko ina jin tsoro? Na ce I ina jin tsoro.

Sai ya ce: “Ruhun tsoro ba daga gare Ni ba ne ko kuwa daga wurin Ubana, amma daga wurin ibilis ne. Tsoro zai iya sa ki kiyi abubuwan da zai kai ki jahannama.”

Babu wanda zai gamshi Ubangiji Allah ba tare da bangaskiya ba, tsoro yana hana bangaskiya. Allah kuwa ba ya son masu tsoro domin ya na rusa bangaskiyar mu. A duk lokacin da muke tafiya Ya na gefe na amma da muka isa jahannama ya rike hannuna a duk lokacin da muke wajen. Na yi murna da Ubangiji ya rike hanuna domin ya cire mani kowace irin tsoro. Wajen na nan kamar na da; babu abin daya chanza, kudan, tsutsotsin, zafin, warin, da kuma kasusuwan, da ihun duk suna nan kamar na da. Mun shiga ta wannan mummunar kofar, sai Ubangiji ya kai ni zuwa wata kashi na mutane. Akwai mutane dayawa da na sani a lokacin da suke duniya. Mutanen suna cikin yanayin tausayi da wahala da kuma azaba amma abu mafi tausayi game da su shi ne yadda fuskokin su ya nuna basu da begen wanni mai taimako.

Ubangiji ya nuna mani wata mata wadda na waye a lokacin da take da rai. Matan ta rasu a dalilin hatsarin mota a farkon shekarar 2005. Na ji mamakin ganin wannan matan a jahannama, domin, kowa ya san cewa ita mace ne mai tsoron Allah, ta na da kaunar Allah kuma. Ubangiji ya ce mani wannan matan ta kaunace shi, shi ma ya kaunace ta, ta bauta masa a lokacin da ta ke a duniya, ta jawo mutane dayawa zuwa ga tuba, ta kuma san maganar Allah sosai. Ta na taimaka wa talakawa da kuma masu bukata, ta taimaka masu a hanyoyi dayawa. Ita baiwa ce mai kirki a hanyoyi dayawa.

Kalmomin da Ubangiji ya gaya mani ya razana ni, sai na tambaye shi me ya sa zai bar mutumin da ya bauta masa ya shiga jahannama. Ubangiji ya kale ni, ya ce wannan matan ta yarda da rudu irin na shaidan. Ko da shi ke ta san maganar Allah sosai, amma ta yarda da karyar shaidan ce wa akwai babba da karamar zunubi. Tayi zato ce wa karamar zunubi ba za ta kai ta ga jahannama ba, domin ita Krista ce.

Ubangiji ya cigaba da ce wa: “a lokatai da dama ina ziyartar ta, ina gaya mata ce wa ta daina abinda ta ke yi amma a tunanin ta abinda ta ke yi karamar zunubi ne, galgadin da na ba ta kuwa ta ce zuciyar ta ce ke ba ta dauki abinda ta ke yi ba. Akwai lokacin da ta daina amma ta gamsar da kanta cewa gargadin ba daga wuri Na ba ne, amma zuciyarta ne domin wannan zunubi ba za ya bata wa Ruhu Mai Tsarki rai ba.”

Na tambayi Ubangiji ya gaya mani irin zunubin da wannan macen ta yi. Sai Ya amsa mani da cewa, “wannan macen ta na da kawa wata nas (mai aikin jinya) ce a asibitin Oshakati. Duk locacin da matan nan batta da lafiya ba za ta je asibiti ta yanki kati ba amma sai ta yi waya ta ce wa kawar ta a shirya mata magani daga dakin magani na asibiti. Kawar ta sai ta bata lokacin da za ta zo ta karbi magungunan. A farko dai ta yarda da karyar shaidan ce wa akwai babbar da karamar zunubi, ta ki gaskiya, ta kuma saka kawarta ta taimake ta cikin zunubin, amma mafi girma shi ne ta yi zunubi a gaban Ruhu Mai Tsarki. Wannan abu ne ya kawo ta jahannama. Ko da ka kawo dubban mutane zuwa ga tuba akwai halin da za ka bata wa Ruhu Mai Tsarki rai, sai ki yi hankali kada ki damu da ceton wasu ki manta da ran ki. Ki kasa kunne ga Ruhu Mai Tsarki a kowanne lokaci.” Bayan da Ubangiji ya gama fada ma ni wannan sai ya ce mani in koma. Krista da dama sukan sami wannan labara da damuwa saisu tambaye ni jinkai da alherin Ubangiji fa? Mutum zai iya rasa cetonsa bayan ya sami ceto? Kamar yadda na fadi a wani waje a litafin nan ba wai ina kawo sabuwar koyaswa ba ne, ina gaya maku abin da Ubangiji ya nuna mani ya kuwa koya mani – da kuma abubuwan daya bar ni in fuskanta. Sai ku dubi amsoshin tambayoyin ku a littafi Mai Tsarki, ku kuma sharanta kan ku.

“Ina dandakin jikina, ina kaishi cikin bauta: domin kada ya zama bayan da na yi ma wadansu wa’azi, ni da kaina yashe ni” (1Korintiyawa 9:27)

“Mi za mu ce fa? Zamu lizima cikin zunubi, domin alheri shi yawaita? Dadai! Mu da muka mutu ga zunubi, kaka zamu kara rayuwa a ciki? (Romawa 6:1-2)

“Kada zunubi fa ya yi mulki cikin jikin ku mai-mutuwa da za ku biye ma sha’awoyinsa” (Romawa 6:12)

“Gama idan muna yin zunubi da nufin zuciyar mu bayan da mun karbi sanin gaskiya, babu sauran wata hadaya domin zunubai, sai sauraro mai ban tsoro ga shari’a, da zafin wuta wadda za ta chinye magabta” (Ibraniyawa 10:26-27)

Zai yiwu in shiga jahannama bayan da na yi bautar Ubangiji na kuma kawo mutane ga tuba? Sai ku sharanta kanku.

RASHIN BIYAYYA

A ranar litinin shida ga watar Mayu ta 2006 agogo mai kara ta tashe ni a karfe biyar da rabi na safe. Da na tsuguna in yi addu’a sai na ji Ruhu Mai Tsarki ya sauko mani, jiki na ya mutu, ya na rawa, ina ji kamar wutar lantarki tana yawo a jikina.

Da rana ina kwance a kan gado na, sai na ga haske ta cika daki, sai na ga wasu fararen abubuwa kamar jigida ma su girmar bakin allura suna fado wa kamar ruwan sama, suna shiga fata na. Bugu da kari na ga wani abu kamar gajemare yana saukowa daga sama, ya sauko ya cika dakin yana kuwa shiga cikin fata ta. Bayan haka sai na ga Yesu yana tahowa waje na a cikin gajemaren. Sai Ya zauna a kujera a gefen gado na kamar yadda yake faruwa, kujeran yakan bayana ne a lokacin da Yake so Ya zauna. Kyakkyawar kujera ce wadda aka yi da zinari, kujerar tana nan kamar kowanne irin kujera mai baya amma a kowanne kafafun kujerar akwai tauraruwar azurfa, akwai irin tauraruwar a bayan kujerar. Kafafuwan kujerar suna na kamar kafar tayar keke. Yesu ya yi mani gaisuwa sai Ya mika mani hannunsa Ya ce in tashi domin lokaci na wuce wa. Ya daga ni da hannu na, na kuwa zauna a bakin gado. Sai Ya ce mani, Victoria mu yi addu’a”. Ya yi addu’a a yaren da ban fahimta ba, ‘amin’ ne kadai ne na gane. Sai Ya tambaye ni me nake gani? Sai nace ina ganin mutane suna tafiya wajen ayukan su, wasu kuma suna isa wajen aiki. Na ga wannan bayan ruwan fararen duwatsun sun daina saukowa.

Na kuma ga kashi-kashin mutane suna zuwa majami’u ranar lahadi da safe sai Ya yi mani bayani cewa: “Wannan wahayi na nufin cewa a duk lokacin daya kamata ki kasance a wani wuri, kin kuma san lokacin da ya kamata ki zama a wurin, akwai mala’iku da suke raba albarku. Idan kin isa a kan lokaci za ki karbi albarkun ki amma idan kin yi latti ba za ki sami albarka ba a ranar domin a daidai lokacin ne mala’ikun suke raba albarkun. Victoria ina son in ja miki kunne game da zuwa wajen aiki da latti, kina yawan zuwa sujada da latti kuma kina yin latti ba tare da kwakkwarar dalili ba, har abada kin rasa wadannan albarkun, ba za su taba dawowa ba. Victoria, ya kamata ki daina wannan abu sai dai idan kina da dalili mai kyau.”

Da Ubangiji Ya fadi wannan sai na ji kamar in bacce daga wurin ko kuwa in ba Shi kyakkyawar dalilin rashin da’a na. Sai na ce Masa wata rana barci ne ya kan dauke ni amma Ya dube ni a cikin idona Ya ce karya nake yi, na kan so ne in koma barci bayan na tashi a maimako in yafe barci na wasu ‘yan mintoci. Bayan Yesu Ya yi mani galgadi sai Ya ce: “Ki tashi mu tafi lokaci na wucewa kuma akwai abubuwa dayawa da ya kamata mu yi”

Ubangiji ya kai ni wani wurin da ban taba zuwa ba, ba mu kuma taba bin hanyar ba. Sai muka isa wata gona cike da kyawawan furanni da kyawawan itatuwa wadda ganyen su duk kore ne, babu wani waje a duniyan nan da za a kwatanta shi da wannan wuri. Furannin suna da launi dabam-dabam masu kyau. Sai muka zauna a wata kujerar gona mai kyau wadda aka yi ta da zinari da wasu kananan taurari na azurfa masu walkiya.

Da muka zauna, Ya ce mani, “Victoria ki kalla, kin ga wancan birnin?” Dana duba sai na ga wata babbar birni mai haske, kyaunta fiye da abin kwatanci. Kofar garin an yi ta da zinari mai walkiya. A kofar akwai wani tsohon mutum, ya na da farar doguwar gemu da kuma farar suma. Na taba ganin wannan mutumin sai na tambayi Yesu wannene wannan mutumin? Sai Ya ce mani Ibrahim ne uban bangaskiya.

Na ga hanyoyi dayawa a cikin wannan birnin wadda aka yi su da zinari, akwai dogayen gine-gine wadda suke yalki kamar zinari. Walkiyar birnin nan ba abun kwatanci bane.

Yesu ya juya ya tambayi ne, “Menene tunanin ki game da wannan birnin?”

Na amsa na ce birnin na da kyau, ina so in je wurin. Yesu Ya ce mani: “zan kai ki wurin idan kin cigaba da yi mani biyayya, gidan ki zai zama a wurin. Sai ki cigaba da biyayya domin idan ki na rashin biyayya, Victoria hankaka za su yi yawo a kan gidan ki, zai kuma zama wajen zama duji da kuma wajen wasan fatalwa.”

Yesu na kaunar mu, kaunar Sa ba za mu iya kwatanta wa ba. Babbar bukatar Sa shi ne mu yi rayuwa har abada da Shi. Baya jin dadin mutanen da suke mutuwa suke zuwa jahannama domin sun ki su karbi ceto wanda Ya basu amma sun zabi mutuwa.

Ko da kai Krista ne wanda an sake haihuwar sa, a kullum ka tuna da wannan abu daya: LOKACI NA WUCEWA